Al-Muminoon 23:71
المؤمنونوَلَوِ ٱتَّبَعَ ٱلْحَقُّ أَهْوَآءَهُمْ لَفَسَدَتِ ٱلسَّمَـٰوَٰتُ وَٱلْأَرْضُ وَمَن فِيهِنَّ ۚ بَلْ أَتَيْنَـٰهُم بِذِكْرِهِمْ فَهُمْ عَن ذِكْرِهِم مُّعْرِضُونَ
Kuma dã gaskiya (Alƙur'ãni) yã bi son zuciyoyinsu, haƙĩƙa dã sammai da ƙasa da wanda yake a cikinsu sun ɓãci. Ã'a, Mun tafo musu da ambaton[1] (darajar) su, sa'an nan sũ daga barin ambaton su mãsu bijirẽwa ne, bijirẽwa.
[1] Zikiri a nan, shi ne Alƙur'ãni wanda ya zo wa Lãrabãwa kõ Ƙuraishawa da abũbuwa na ɗaukakarsu, da ambatonsũnansu, da shiryar da su, da gabãtar da su a kan sauran kabĩlu. Amma duk da haka sunã bijirewa daga gare Shi.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net