Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 23 · Aya ta 20

Al-Muminoon 23:20

المؤمنون

وَشَجَرَةً تَخْرُجُ مِن طُورِ سَيْنَآءَ تَنۢبُتُ بِٱلدُّهْنِ وَصِبْغٍ لِّلْـَٔاكِلِينَ

Ma’ana

Da wata itãciya,[1] tanã fita daga dũtsin Sainã'a, tanã tsira da man shãfãwa, da man miya dõmin masu cĩ.

[1] Itãciyar Zaitũni. Ita ce itãciyar farko da ta tsira a kan ƙasa a bãyan Ɗũfãna tanã rãyuwa mai dõgon lõkaci; an ce tanã rãyuwa kamar shekara dubũ huɗu. Anã cin 'ya'yanta, anã man shãfãwa da su, kuma anã yin miya dasu. Asalin sibg, rini dõmin tanã rina lõmar tuwo. Dũtsen Sĩnã'a mai albarka, ɗũr, shĩ ne dũtSe mai itãce a kansa.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Muminoon

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net