Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 22 · Aya ta 41

Al-Hajj 22:41

الحج

ٱلَّذِينَ إِن مَّكَّنَّـٰهُمْ فِى ٱلْأَرْضِ أَقَامُوا۟ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَوُا۟ ٱلزَّكَوٰةَ وَأَمَرُوا۟ بِٱلْمَعْرُوفِ وَنَهَوْا۟ عَنِ ٱلْمُنكَرِ ۗ وَلِلَّهِ عَـٰقِبَةُ ٱلْأُمُورِ

Ma’ana

Waɗanda suke idan Muka bã su ĩko a cikin ƙasa sai su tsai da salla, kuma su baybr da zakka kuma su yi umurni da abin da aka sani,[1] kuma su hana daga abin da ba a sani ba. Kuma ãƙibar al'amura ga Allah take.

[1] Abin da aka sani daga shar'ia watau shĩ ne alheri, kuma abin da ba a sani ba ga shari'a, watau sharri wanda Allah bã Ya so, akasin alheri. Tsayar da ayyukan alheri ba zai isa ba sai anã yin wa'azi ga mutãne a umarce su da yin alhħri kuma a hana su daga aikata sharri.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Hajj

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net