Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 22 · Aya ta 25

Al-Hajj 22:25

الحج

إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ وَيَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ وَٱلْمَسْجِدِ ٱلْحَرَامِ ٱلَّذِى جَعَلْنَـٰهُ لِلنَّاسِ سَوَآءً ٱلْعَـٰكِفُ فِيهِ وَٱلْبَادِ ۚ وَمَن يُرِدْ فِيهِ بِإِلْحَادٍۭ بِظُلْمٍ نُّذِقْهُ مِنْ عَذَابٍ أَلِيمٍ

Ma’ana

Lalle ne waɗanda suka kãfirta kuma suka taushe (mutãne) daga hanyar Allah da masallaci mai alfarma wanda Muka sanya shi ga mutãne alhãli kuwa mazauni a ciki da baƙauye daidai suke kuma wanda ya yi nufin karkatar[1] da gaskiya a cikinsa da zãlunci zã Mu ɗanɗana masa daga wata azãba mai raɗadi.

[1] Ilhãdi, shĩ ne yin ibãda bã yadda Allah Ya yi umurni da a yi ta ba. Wanda ya yi nufin karkatar da gaskiyar ibãda a cikin hurumin Makka, Allah zai yi masa azãba mai tsanani,balle fa a ce mutum ya aikata. Sabõda haka yanã wajaba ga mai nufin zuwa Hajji ya kõyi yadda ake yin ibãda kãfinya tafi Makka dõmin kada ya jãwo wa kansa halaka.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Hajj

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net