Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 22 · Aya ta 19

Al-Hajj 22:19

الحج

هَـٰذَانِ خَصْمَانِ ٱخْتَصَمُوا۟ فِى رَبِّهِمْ ۖ فَٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ قُطِّعَتْ لَهُمْ ثِيَابٌ مِّن نَّارٍ يُصَبُّ مِن فَوْقِ رُءُوسِهِمُ ٱلْحَمِيمُ

Ma’ana

waɗannan ƙungiyõyi biyu[1] ne mãsu husũma, sun yi husũma ga sha'anin Ubangijinsu. To, waɗanda suka kãfirta an yanka musu waɗansu tufafi daga wata irin wuta, anã zuba tafasasshen ruwa daga bisa kãwunansu.

[1] Kuma ya kasa mutãne ƙungiya biyu, ƙungiyar farko sũne mãsu bin addinin gaskiya, ƙungiya ta biyu sũ ne mãsu karkace wa addinin gaskiya, kamar kasũsuwa uku na farko. A kõ da yaushe akwai husũma a tsakãnin ƙungiyoyin biyu. Sa'an nan ya ambaci sakamakon ƙungiyar ƙarya ta farkon,.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Hajj

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net