Al-Hajj 22:17
الحجإِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَٱلَّذِينَ هَادُوا۟ وَٱلصَّـٰبِـِٔينَ وَٱلنَّصَـٰرَىٰ وَٱلْمَجُوسَ وَٱلَّذِينَ أَشْرَكُوٓا۟ إِنَّ ٱللَّهَ يَفْصِلُ بَيْنَهُمْ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ شَهِيدٌ
Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni da waɗanda suka tũba (Yahũdu) da waɗanda suka karkace (Saba'ãwa) da Nasãra da Majũsãwa da waɗanda suka yi shirka, lalle ne Allah Yanã yin hukunci a tsakãninsu a Ranãr ¡iyãma. Lalle ne Allah Mahalarci ne a kan dukkan kõme[1].
[1] Anã ce wa Yahũdãwa 'waɗanda suka tũba,' dõmin sun sãɓã wa maganar Annabinsu,Mũsã, wanda ya ce wa Allah,"Mun tũba zuwa gare Ka." Saba'ãwa su ne mãsu bauta wa malã'iku daga cikin Lãrabãwa ko Yahũdãwa. Nasãra sũ ne waɗanda suka bi Annabi Ĩsa Ɗan Maryamu, amincin Allah ya tabbata a gare shi. Majũsãwa sũ ne mãsu bautã wa wuta da irin addinin Fãrisa. Mãsu shirki, su ne mãsu bauta wa, gumãka kõ aljannu kõ waɗansu mutãne, wãtau irin addinin Lãrabãwa na lõkacin Jãhiliyya da irin bautar da waɗansu Musulmi ke yi wa waliyyai a yanzu.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net