Al-Anbiyaa 21:98
الأنبياءإِنَّكُمْ وَمَا تَعْبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ حَصَبُ جَهَنَّمَ أَنتُمْ لَهَا وَٰرِدُونَ
(A ce musu) "Lalle ne, kũ da abin[1] da kuke bautãwa, baicin Allah makãmashin Jahannama ne. Kũ mãsu tusgãwa gare ta ne."
[1] Bãyin Allah sãlihai da malãiku waɗanda waɗansu mutãne suka bauta musu da tsammãnin cewa zã su cecesu daga Allah, bã zai sanya su Wuta ba sabõda ibãdar da aka yi musu, dõmin yabon Allah yã rigãyi hushinsa zuwa gare su. Bãyansu da mai bautar da wanda ake bautawar kamar gumãka da waɗansunsu, Wuta za su shiga.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net