Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 21 · Aya ta 91

Al-Anbiyaa 21:91

الأنبياء

وَٱلَّتِىٓ أَحْصَنَتْ فَرْجَهَا فَنَفَخْنَا فِيهَا مِن رُّوحِنَا وَجَعَلْنَـٰهَا وَٱبْنَهَآ ءَايَةً لِّلْعَـٰلَمِينَ

Ma’ana

Kuma da wadda ta tsare farJinta daga alfãsha. Sai Muka hũra a cikinta daga rũhinMu.[1] Kuma Muka sanya ta ita da ɗanta wata ãyã ga dũniya.

[1] Rũhin Allah a nan, shi ne Malã'ika jibrĩla. Shĩ ne ya hũra a cikin wuyan rĩgarta, sai ta yi cikĩ da Ĩsã. Maryamu bã Annabiya ba ce, an ambace ta ne dõmin shimfiɗa ga maganar Ĩsã, amincin Allah ya tabbata a gare Shi. Zamanta ãyã shi ne ta sãmi ɗã bãda namiji ba, kuma wanda ya yi haƙuri ga tsaron haddojin Allah, Allah zai ɗaukaka shi da ni'imar dũniya da ta Lãhira. Ɗanta ya zama ãyã sabõda magana yana yãro, da Annabci da ɗaukar haƙuri ga zartar da umurnin Allah.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Anbiyaa

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net