Al-Anbiyaa 21:84
الأنبياءفَٱسْتَجَبْنَا لَهُۥ فَكَشَفْنَا مَا بِهِۦ مِن ضُرٍّ ۖ وَءَاتَيْنَـٰهُ أَهْلَهُۥ وَمِثْلَهُم مَّعَهُمْ رَحْمَةً مِّنْ عِندِنَا وَذِكْرَىٰ لِلْعَـٰبِدِينَ
Sai Muka karɓa masa, sa'an nan Muka kuranye abin da ke a gare shi na cũta, kuma Muka kãwo masa mutãnesa da kwatank wacinsu tãre da su, sabõda rahama daga wurin Mu da tunãtarwa[1] ga mãsu ibãda.
[1] Ayyuba Manzon Allah, an jarrabe shi da wahalõlĩ ga jikinsa da halakar ɗiyansa ya yi haƙuri da hukuncin Allah, sai Allah Ya mayar masa da abin da ya halaka, sa'an nankuma ya ƙãrã masa wani kamarsa, dõmin rahamarSa ga mãsu mayar da al'amari a gare shi, da kuma wa'azi ga mãsuibãda dõmin kada aukuwar wata masĩfa ta sanya su kãtsewa da rashin ɗaukar haƙuri.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net