Al-Anbiyaa 21:105
الأنبياءوَلَقَدْ كَتَبْنَا فِى ٱلزَّبُورِ مِنۢ بَعْدِ ٱلذِّكْرِ أَنَّ ٱلْأَرْضَ يَرِثُهَا عِبَادِىَ ٱلصَّـٰلِحُونَ
Kuma lalle haƙĩƙa Mun rubũta a cikin Littãfi baicin Ambato[1] (Lauhul Mahfũz) cẽwa ƙasã, bayĩna sãlihai, sunã gãdonta.
[1] Allah Yanã mallakar da ƙasa bãyinsa sãlihai, bã zã ta fita daga gare su ba sai idan sun musanya addininsu na ƙwarai da wani mugu.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net