Taa-Haa 20:83
طهوَمَآ أَعْجَلَكَ عَن قَوْمِكَ يَـٰمُوسَىٰ
"Kuma mẽne ne ya gaggautar[1] da kai ga barin mutãnenka? Yã Mũsã!"
[1] Mũsã ya zãɓi mutun sabã'in daga Banĩ Isrã'ĩla, dõmin su tafi wurin Mĩƙãti tãre, su ji maganar Ubangiji. A lõkacin da ya yi kusa, sai ya yi gaggãwa dõmin bege. Kõ kuwa a bãyan azumin kwãna arba'in ya tafi a wurin Mĩƙãtin, Allah Ya fãra yi masa magana game da mutãnensa dõmin ɗebe masa kewa. Sai ya karɓa da cewa, "Sunã nan a kan sãwũna." Wãtau sunã nan a kan abin da na ɗõra su a kansa na addini da aƙĩda ta tauhĩdi. Sai Allah Ya ce masa "A'aha! sun musanya addininka da bautar maraƙi.".
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net