Taa-Haa 20:18
طهقَالَ هِىَ عَصَاىَ أَتَوَكَّؤُا۟ عَلَيْهَا وَأَهُشُّ بِهَا عَلَىٰ غَنَمِى وَلِىَ فِيهَا مَـَٔارِبُ أُخْرَىٰ
Ya ce: "Ita sandãta ce, inã dõgara a kanta, kuma inã kakkaɓar ganye da ita a kan ƙananan bisãshẽna kuma inã da waɗansu bukãtõci[1] na dabam a gare ta."
[1] Amfãnõnin sanda: Anã riƙon alkĩbla a cikin daji ta zama sitra, anã dõgara a kanta sabõda gajiya kõ rauni. Lĩmãmin Juma'a na dõgara a kanta a lõkacin huɗuba anã fita da ita a cikin ruwan sama anã dõgara a kanta, anã dũkan iyãli da ita dõmin ladabtarwa. A cikin wani Hadĩsi Annabi ya ce: "Ka rãtaye sandarka inda iyãlinka suke ganin ta." Riƙon sanda na sanya farkawa gabarin dũniya, watau mai ita ya zama a cikin hãlin tafiya.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net