Taa-Haa 20:117
طهفَقُلْنَا يَـٰٓـَٔادَمُ إِنَّ هَـٰذَا عَدُوٌّ لَّكَ وَلِزَوْجِكَ فَلَا يُخْرِجَنَّكُمَا مِنَ ٱلْجَنَّةِ فَتَشْقَىٰٓ
Sai Muka ce: "Ya Ãdamu! Lalle ne wannan maƙiyi[1] ne gare ka da kuma ga mãtarka, sabõda haka kada ya fitar da ku daga Aljanna har ku wahala."
[1] Anã farkar da ɗiyan Ãdamu ga maƙiyin ubansu wanda ya sabbaba musu wahalar zuwa dũniya da haɗuwa da taklĩfi a cikinta. Kuma bin wannan taklĩfi yanã zame masa sauƙi idan sun bĩ shi yadda Allah Ya ce: amma idan sun bi hanyar Shaiɗan, maƙiyinsu, to, bãbu abin da zai sãmu a gare su fãce ƙãrin wahala daga dũniya har Lãhira.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net