Taa-Haa 20:105
طهوَيَسْـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلْجِبَالِ فَقُلْ يَنسِفُهَا رَبِّى نَسْفًا
Kuma sunã tambayar ka daga duwãtsu[1] sai ka ce: "Ubangijina Yana shẽƙe su shẽƙẽwa,
[1] Ana siffanta duwãtsu maɗaukaka da ayyukan dũniya waɗanda bã ibãdar Allah ba, watau al'adu da ibãdõjin da ba ibãdar Allah ba, dukansu kõme yawansu zã su lãlãce a rãnar da Mai kira, wãtau lsrãfĩl, zai bũsa ƙaho na kiran mutãne zuwa ga Tãshin Ƙiyãma, kira wanda bãbu makarkata daga gare shi, watau bã kamar kiran da Annabãwa suka yi ba, wanda waɗansu mutãne suka karkace daga gare shi a nan dũniya.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net