Al-Baqara 2:91
البقرةوَإِذَا قِيلَ لَهُمْ ءَامِنُوا۟ بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ قَالُوا۟ نُؤْمِنُ بِمَآ أُنزِلَ عَلَيْنَا وَيَكْفُرُونَ بِمَا وَرَآءَهُۥ وَهُوَ ٱلْحَقُّ مُصَدِّقًا لِّمَا مَعَهُمْ ۗ قُلْ فَلِمَ تَقْتُلُونَ أَنۢبِيَآءَ ٱللَّهِ مِن قَبْلُ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ
Kuma idan aka ce musu: "Ku yi ĩmãni da abin da Allah Ya saukar." Sai su ce: "Muna ĩmãni da abin da aka saukar a gare mu," kuma suna kãfircẽwa da abin da ke bãyansa, alhãli kuwa, shi ne gaskiyar (da suka sani) mai gaskatawa ga abin da yake tãre da su (na Attaura) Ka ce: "To, don me kuke kashe annabãwan Allah gabãnin wannan, idan kun kasance mãsu bãyar da gaskiya?"[1]
[1] Waɗannan Annabãwan da kuka kashe ko kuka ƙaryata a cikinku suke kũ ne aka saukar wa da abin da aka bã su, sabõda haka da'awarku ta cewa kunã ĩmãni da abin da aka saukar muku ƙarya ce.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net