Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 2 · Aya ta 83

Al-Baqara 2:83

البقرة

وَإِذْ أَخَذْنَا مِيثَـٰقَ بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ لَا تَعْبُدُونَ إِلَّا ٱللَّهَ وَبِٱلْوَٰلِدَيْنِ إِحْسَانًا وَذِى ٱلْقُرْبَىٰ وَٱلْيَتَـٰمَىٰ وَٱلْمَسَـٰكِينِ وَقُولُوا۟ لِلنَّاسِ حُسْنًا وَأَقِيمُوا۟ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُوا۟ ٱلزَّكَوٰةَ ثُمَّ تَوَلَّيْتُمْ إِلَّا قَلِيلًا مِّنكُمْ وَأَنتُم مُّعْرِضُونَ

Ma’ana

Kuma a lõkacin da Muka karɓi alkawarin Bani-Isrã'ĩla[1]: "Kada ku bauta wa kõwa fãce Allah, kuma ga mahaifa ku kyautata, da mai zumunta da marãyu da matalauta, kuma ku faɗi magana mai kyau zuwa ga mutãne, kuma ku tsayar da salla, kuma ku bãyar da zakka, sa'an nan kuka jũya bãya, fãce kaɗan daga gare ku, alhãli kuwa kuna mãsu bijirẽwa.

[1] Tunãtar da Banĩ Isrã'ĩla alkawurra gõma da Allah Yã yi da Mũsã a cikin Attaura a kansu. Na farko bã zã su bauta wa kõwa ba fãce Allah. Na biyu kyautata wa iyãye da dangi da marãyu da matalauta. Na uku, faɗin magana mai kyau zuwa ga mutãne. Na huɗu, tsayar da salla. Nabiyar, bãyar da zakka. Na shida, bã zã a kashe rai bãbu hakki na sharĩ'a ba. Na bakwai, bã zã a fitar da kõwa daga gidansa ba. Na takwas, bã zã a taimaki azzãlumi a kan zãluncinsa ba. Na tara, idan abõkan gãbã sun kãma wani daga cikinsu, su yi fansarsa. Nagõma, ɗã'a ga kõwane Manzon Allah wanda bai sãɓãwa Attaura ba ga aƙida.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Baqara

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net