Al-Baqara 2:40
البقرةيَـٰبَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ ٱذْكُرُوا۟ نِعْمَتِىَ ٱلَّتِىٓ أَنْعَمْتُ عَلَيْكُمْ وَأَوْفُوا۟ بِعَهْدِىٓ أُوفِ بِعَهْدِكُمْ وَإِيَّـٰىَ فَٱرْهَبُونِ
Yã Banĩ Isrã'Ĩla[1]! Ku tuna ni'imãTa a kanku, kuma ku cika alƙawariNa, In cika muku da alƙawarinku. kuma Ni, ku ji tsõro Na.
[1] Bãyan kiran mutãne gabã ɗaya zuwa ga addinin musulunci, sai kuma ya keɓance Yahũdu da kira zuwa ga addinin, dõmin sun bambanta da sauran kãfirai, sabõda ilminsu ga gaskiyar Musulunci. Yã gabata cewa jama'ar, kashi huɗu ce; mũminai, da kãfiran Lãrabãwan da bã zã su musulunta ba, da munãfukai da Yahũdu. Ya kira Yahũdu da Bani Isrã'ĩla, dõmin Ya tunãtar da su, cewa anã kiransu ne zuwa ga addini irin na ubansu Ya'aƙũbu bawan Allah.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net