Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 2 · Aya ta 275

Al-Baqara 2:275

البقرة

ٱلَّذِينَ يَأْكُلُونَ ٱلرِّبَوٰا۟ لَا يَقُومُونَ إِلَّا كَمَا يَقُومُ ٱلَّذِى يَتَخَبَّطُهُ ٱلشَّيْطَـٰنُ مِنَ ٱلْمَسِّ ۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ قَالُوٓا۟ إِنَّمَا ٱلْبَيْعُ مِثْلُ ٱلرِّبَوٰا۟ ۗ وَأَحَلَّ ٱللَّهُ ٱلْبَيْعَ وَحَرَّمَ ٱلرِّبَوٰا۟ ۚ فَمَن جَآءَهُۥ مَوْعِظَةٌ مِّن رَّبِّهِۦ فَٱنتَهَىٰ فَلَهُۥ مَا سَلَفَ وَأَمْرُهُۥٓ إِلَى ٱللَّهِ ۖ وَمَنْ عَادَ فَأُو۟لَـٰٓئِكَ أَصْحَـٰبُ ٱلنَّارِ ۖ هُمْ فِيهَا خَـٰلِدُونَ

Ma’ana

Wadanda suke cin ribã[1] ba su tashi, fãce kamar yadda wanda da Shaiɗan yake ɗimautarwa daga shafa yake tashi. Wancan, dõmin lalle ne sun ce: "Ciniki kamar riba yake."Kuma Allah Ya halatta ciniki kuma Ya haramta riba. To, wanda wa'azi daga Ubangijinsa, ya je masa, sa'an nan ya hanu, to yana da abin da ya shige, kuma al'amarinsa (ana wakkala shi) zuwa ga Allah. Kuma wanda ya kõma, to, waɗannan sũ ne abõkan Wuta, sũ a cikinta madawwama ne.

[1] Ribã ita ce ƙãri ga adadi koga lõkaci. Amma ƙãrin adadi shi ne ƙãri a cikin mu'ãmala da zinãri da azurfa da abũbuwan ci ga rayuwa. Yana haramta ga jinsi guda kawai, kuma ana sharɗantawa ga abinci ya zama abinci kõ abin gyaransa, kuma anã iya ajiye shi, ban da 'ya'yan itãcen marmari da duma da ruwa. Amma ga jinkiri an hana riba muɗlaƙan. kõ dã ga 'ya'yan itãcen marmari. Takardun kuɗi kamar sil'õ'i suke dõmin haka ƙimarsu tana hawa kuma tanã sauka. Har yanzu malamai ba su yanke hukunci a kansu ba sõsai. Annabi, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Ka bar abin da yake sanya maka shakka zuwa ga wanda ba ya sanya maka shakka.".

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Baqara

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net