Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 2 · Aya ta 268

Al-Baqara 2:268

البقرة

ٱلشَّيْطَـٰنُ يَعِدُكُمُ ٱلْفَقْرَ وَيَأْمُرُكُم بِٱلْفَحْشَآءِ ۖ وَٱللَّهُ يَعِدُكُم مَّغْفِرَةً مِّنْهُ وَفَضْلًا ۗ وَٱللَّهُ وَٰسِعٌ عَلِيمٌ

Ma’ana

Shaiɗan yana yi muku alƙawarin talauci, kuma yana umurnin ku da alfasha[1], kuma Allah Yana yi muku alƙawarin gãfara daga gare shi da ƙãri, kuma Allah Mawadãci ne, Masani.

[1] Alfãsha ita ce ayyukan zunubi kamar zina da shan giya, alhãli ɓatar da dũkiya a nan, ya fi tsanani, kuma bãbu wani badali don sakamako, sabõda haka ƙin ciyarwa dõmin gudun talauci da umurninku da alfãsha sun sãɓã wa jũna, ga abin da shi Shaiɗan yake gaya muku; watau kada ku ciyar, dõmin gudun talauci, amma ku sha giya, ku yi zina!.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Baqara

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net