Al-Baqara 2:26
البقرةإِنَّ ٱللَّهَ لَا يَسْتَحْىِۦٓ أَن يَضْرِبَ مَثَلًا مَّا بَعُوضَةً فَمَا فَوْقَهَا ۚ فَأَمَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ فَيَعْلَمُونَ أَنَّهُ ٱلْحَقُّ مِن رَّبِّهِمْ ۖ وَأَمَّا ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ فَيَقُولُونَ مَاذَآ أَرَادَ ٱللَّهُ بِهَـٰذَا مَثَلًا ۘ يُضِلُّ بِهِۦ كَثِيرًا وَيَهْدِى بِهِۦ كَثِيرًا ۚ وَمَا يُضِلُّ بِهِۦٓ إِلَّا ٱلْفَـٰسِقِينَ
Lalle ne, Allah bã Ya jin kunyar Ya bayyana wani misãli, kõwane iri ne, sauro da abin da yake bisa gare shi. To, amma waɗanda suka yi ĩmãni, sai su san cewa lalle shi ne gaskiya daga Ubangijin su, kuma amma waɗanda suka kãfirta, sai su ce: "Mẽne ne Allah Ya yi nufi da wannan[1] ya zama misãli?" na ɓatar da wasu mãsu yawa da shi, kuma Yana shiryar da wasu mãsu yawada shi, kuma bã Ya ɓatarwa da shi fãce fasiƙai.
[1] Misãli da kamar mãtan Aljanna mãsu tsarki. Ba mãtã ba kõ da sauro ko abin da ya fi, kõ ya kãsa sauro, to, akwai hikima a cikin halittarsa, wadda zã ta jãwo hankalin mai hankali ga ĩmãni da Allah sabõda ita.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net