Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 2 · Aya ta 259

Al-Baqara 2:259

البقرة

أَوْ كَٱلَّذِى مَرَّ عَلَىٰ قَرْيَةٍ وَهِىَ خَاوِيَةٌ عَلَىٰ عُرُوشِهَا قَالَ أَنَّىٰ يُحْىِۦ هَـٰذِهِ ٱللَّهُ بَعْدَ مَوْتِهَا ۖ فَأَمَاتَهُ ٱللَّهُ مِا۟ئَةَ عَامٍ ثُمَّ بَعَثَهُۥ ۖ قَالَ كَمْ لَبِثْتَ ۖ قَالَ لَبِثْتُ يَوْمًا أَوْ بَعْضَ يَوْمٍ ۖ قَالَ بَل لَّبِثْتَ مِا۟ئَةَ عَامٍ فَٱنظُرْ إِلَىٰ طَعَامِكَ وَشَرَابِكَ لَمْ يَتَسَنَّهْ ۖ وَٱنظُرْ إِلَىٰ حِمَارِكَ وَلِنَجْعَلَكَ ءَايَةً لِّلنَّاسِ ۖ وَٱنظُرْ إِلَى ٱلْعِظَامِ كَيْفَ نُنشِزُهَا ثُمَّ نَكْسُوهَا لَحْمًا ۚ فَلَمَّا تَبَيَّنَ لَهُۥ قَالَ أَعْلَمُ أَنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ قَدِيرٌ

Ma’ana

Kõ kuwa[1] wanda ya shũɗe a kan wata alƙarya, alhãli kuwa tana wõfintacciya a kan gadãjen rẽsunanta. Ya ce: "Yaya Allah zai rãyar da wannan a bãyan mutuwarta." Sai Allah Ya matar da shi, shẽkara ɗari; sa'an nankuma ya tãyar da shi. Ya ce: "Nawa ka zauna?" Ya ce: "Na zauna yini ɗaya ko kuwa rabin yini." Ya ce: "A'a kã zauna shẽkara ɗari." To, ka dũba zuwa ga abincinka, da abin shanka, (kõwanensu) bai sãke ba, kuma ka dũba zuwa ga jãkinka, kuma dõmin Mu sanya ka wata ãyã ga mutãne. Kuma ka duba zuwa ga ƙasũsuwa yadda Muke mõtsarda su sa'an nan kuma Mu tufãtar da su, da nãma", To, a lõkacin da (abin) ya bayyana a gare shi, ya ce: "Ina sanin cẽwa lalle Allah a kan dukan kõme Mai ĩkõn yi ne."

[1] Ƙissa ta biyu Uzairu da alƙarya matacciya, da jãkinsa, da abincinsa bãyan shekara ɗari.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Baqara

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net