Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 2 · Aya ta 254

Al-Baqara 2:254

البقرة

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ أَنفِقُوا۟ مِمَّا رَزَقْنَـٰكُم مِّن قَبْلِ أَن يَأْتِىَ يَوْمٌ لَّا بَيْعٌ فِيهِ وَلَا خُلَّةٌ وَلَا شَفَـٰعَةٌ ۗ وَٱلْكَـٰفِرُونَ هُمُ ٱلظَّـٰلِمُونَ

Ma’ana

Ya ku waɗanda[1] suka yi ĩmãni! Ku ciyar daga abin da Muka azurta ku daga gabãnin wani yini ya zo bãbu ciniki a cikinsa kuma bãbu abũta, kuma bãbu cẽto, kuma kãfirai sũ ne Azzãlumai.

[1] Bãyan tabbatar da manzancin Annabi Muhammadu tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, sa'an nan ya sãbunta fuskanta da kira zuwa ga waɗanda suka yi ĩmãni da Annabi, kuma ya farkar da su game da zuwan babbar rãna ta Ƙiyãma. Sa'an nan ya faɗi sũnanSa Ta'ãla, Allah Mai sifõfin da ke cikin ãyã ta 255.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Baqara

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net