Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 2 · Aya ta 248

Al-Baqara 2:248

البقرة

وَقَالَ لَهُمْ نَبِيُّهُمْ إِنَّ ءَايَةَ مُلْكِهِۦٓ أَن يَأْتِيَكُمُ ٱلتَّابُوتُ فِيهِ سَكِينَةٌ مِّن رَّبِّكُمْ وَبَقِيَّةٌ مِّمَّا تَرَكَ ءَالُ مُوسَىٰ وَءَالُ هَـٰرُونَ تَحْمِلُهُ ٱلْمَلَـٰٓئِكَةُ ۚ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً لَّكُمْ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ

Ma’ana

Kuma annabinsu ya ce musu: "Lalle ne alãmar mulkinSa ita ce akwatin[1] nan ya zo muku, a cikinsa akwai natsuwa daga Ubangijinku da sauran kaya daga abin da Gidan Mũsã da Gidan Hãrũna suka bari malã'iku suna ɗaukarsa. Lalle ne a cikin wancan akwai alãma a gare ku (ta naɗin ¦ãlũta daga Allah ne) idan kun kasance mãsu ĩmãni."

[1] Akwatin Natsuwa, an saukar da shi tãre da Ãdam a cikinsa akwai sũrõrin annabãwa, da gãdon riƙonsa ya kai ga Mũsã yanã sanya Attaura a ciki sabõda haka aka sãmi karyayyun allunan Attaura a ciki da rawanin Harũna da wani abu daga Mannu da Salwa. A lõkacin da Amãliƙa suka rinjãye su, sai suka karɓe wannan akwãti suka ajiye shi inda bai dãce da shi ba, har a lõkacin da malã'iku suka ɗauke shi zuwa ga Ɗãlũta.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Baqara

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net