Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 2 · Aya ta 245

Al-Baqara 2:245

البقرة

مَّن ذَا ٱلَّذِى يُقْرِضُ ٱللَّهَ قَرْضًا حَسَنًا فَيُضَـٰعِفَهُۥ لَهُۥٓ أَضْعَافًا كَثِيرَةً ۚ وَٱللَّهُ يَقْبِضُ وَيَبْصُۜطُ وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ

Ma’ana

Wãne ne wanda[1] zai bai wa Allah rance, rance mai kyau, dõmin Ya riɓanya masa, riɓanyãwa mai yawa? Kuma Allah Shi ne ke damƙewa, kuma yana shimfiɗawa, kuma zuwa a gare Shi ake mayar da ku.

[1] Bãyãni ga cewa jihãdi bã ya yiwuwa sai mutãne kõwa ya bãyar da taimakonsa na dũkiya kõ na ma'ana. Kuma duk wanda ya bãyar da taimako, to, rance ne ya bai wa Allah, Wanda yake Shi ne Ya bãyar da asalin dũkiyar, da yawa kõ kaɗan, kuma Mai sakamako ga wanda ya yi aiki da umurninSa da babban sakamako, bãyan an kõma zuwa gareShi. Jihãdi wãjibi ne ga tattalin arziki domin tsaro.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Baqara

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net