Al-Baqara 2:215
البقرةيَسْـَٔلُونَكَ مَاذَا يُنفِقُونَ ۖ قُلْ مَآ أَنفَقْتُم مِّنْ خَيْرٍ فَلِلْوَٰلِدَيْنِ وَٱلْأَقْرَبِينَ وَٱلْيَتَـٰمَىٰ وَٱلْمَسَـٰكِينِ وَٱبْنِ ٱلسَّبِيلِ ۗ وَمَا تَفْعَلُوا۟ مِنْ خَيْرٍ فَإِنَّ ٱللَّهَ بِهِۦ عَلِيمٌ
Suna tambayar ka mẽne nezã su ciyar. Ka ce: Abin da kuka ciyar daga alhẽri sai ga mahaifa[1] da mafi kusantar dangantaka da marãyu da matalauta da ɗan hanya. Kuma abin da kuka aikata daga alhẽri, to, lalle ne, Allah gare shi Masani ne.
[1] Ciyar da mahaifa matalauta wãjibi ne haka ɗiya da 'ya'ya ƙanãna waɗanda bãsu da dũkiya har yãro ya balaga a kuma aurar da yãrinya ta tãre a gidan mijinta. Amma mãtar aure da bãwan mutum ciyar da su wãjibi ne kõ dã sunã da dũkiya. Liyãfa ga bãƙo har kwãna uku gwargwadon bukãta wãjibi ne, sauran ciyarwa mustahabbi ce bãyan an fitar da zakka idan tã wajaba.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net