Al-Baqara 2:204
البقرةوَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يُعْجِبُكَ قَوْلُهُۥ فِى ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا وَيُشْهِدُ ٱللَّهَ عَلَىٰ مَا فِى قَلْبِهِۦ وَهُوَ أَلَدُّ ٱلْخِصَامِ
Kuma akwai daga mutãne[1] wanda maganarsa tana bã ka sha'awa a cikin rãyuwar dũniya, alhãli yanã shaidar da Allah a kan abin da yake cikin zuciyarsa, kuma shi mai tsananin husũma ne.
[1] Bayãnin munafuki da hãlayensa, a cikin jama'a, a san shi, dõmin kada a dõgara a kansa. Haka mutumin kirki shi ma ana son a san shi dõmin a dogara da shi kamar yadda yayi bayãninsa.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net