Al-Baqara 2:188
البقرةوَلَا تَأْكُلُوٓا۟ أَمْوَٰلَكُم بَيْنَكُم بِٱلْبَـٰطِلِ وَتُدْلُوا۟ بِهَآ إِلَى ٱلْحُكَّامِ لِتَأْكُلُوا۟ فَرِيقًا مِّنْ أَمْوَٰلِ ٱلنَّاسِ بِٱلْإِثْمِ وَأَنتُمْ تَعْلَمُونَ
Kada ku ci dukiyõyinku[1] a tsakãninku da ƙarya, kuma ku sãdu da ita zuwa ga mahukunta dõmin ku ci wani yanki daga dũkiyõyin mutãne da zunubi alhãli kuwa kũ, kuna sane.
[1] Haramun ne cin dũkiyar mutãne da zãlunci. An haɗa wannan ãyã da ta gabãninta, ta azumi, dõmin haɗin hana ci da ya gama su. Sãduwa da mahukunta da dukiya, shi ne rashawa, Allah Yã la'ani mai bãyar da ita da mai karɓarta.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net