Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 2 · Aya ta 158

Al-Baqara 2:158

البقرة

إِنَّ ٱلصَّفَا وَٱلْمَرْوَةَ مِن شَعَآئِرِ ٱللَّهِ ۖ فَمَنْ حَجَّ ٱلْبَيْتَ أَوِ ٱعْتَمَرَ فَلَا جُنَاحَ عَلَيْهِ أَن يَطَّوَّفَ بِهِمَا ۚ وَمَن تَطَوَّعَ خَيْرًا فَإِنَّ ٱللَّهَ شَاكِرٌ عَلِيمٌ

Ma’ana

Lalle ne Safã da Marwa[1] suna daga wurãren ibãdar Allah, to, wanda ya yi hajin ¦ãki kõ kuwa ya yi Umra, to, bãbu laifi a kansa ga ya yi ɗawãfi gare su, su biyu. Kuma wanda ya ƙãra yin wani aikin alhẽri to, lalle ne Allah Mai gõdiya ne, Masani.

[1] Al'umma bã ta haɗuwa sai an wanke ta daga al'adun Jãhiliyya, har dai waɗanda suka haɗu da ibãda, sabõda haka aka fãra da Safã da Marwa dõmin a ije cewa ɗawãfi a tsakãninsu aikin Jãhiliyya ne, sũ suna cikin ayyukan ibãda da Allah Ya shar'anta kuma ɗawãfin mutãne da sa'ayi a kansu da tsakãninsu duka daidai suke Baƙuraishe da Balãrabe da Ba'ajame duka daidai suke.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Baqara

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net