Al-Baqara 2:147
البقرةٱلْحَقُّ مِن رَّبِّكَ ۖ فَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلْمُمْتَرِينَ
Gaskiya daga Ubangijinka[1] take sabõda haka, lalle kada ka kasance daga mãsu shakka.
[1] Jũyãwar alƙibla abu ne na gaskiya daga Allah dõmin rarrashin wanda Allah bai yi nufi da tsĩrarsa ba ya ƙãre. Bãyan rarrashi sai yankewa wannan shi ne matakin farko da Musulmi suka fara tsiraita da shi daga maƙiyansu bayyane. Yanzu kuma Musulmi sun zama dabam.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net