Al-Baqara 2:14
البقرةوَإِذَا لَقُوا۟ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ قَالُوٓا۟ ءَامَنَّا وَإِذَا خَلَوْا۟ إِلَىٰ شَيَـٰطِينِهِمْ قَالُوٓا۟ إِنَّا مَعَكُمْ إِنَّمَا نَحْنُ مُسْتَهْزِءُونَ
Kuma idan sun haɗu da waɗanda suka yi ĩmãni, sukan ce: "Mun yi ĩmãni. "Kuma idan sun wõfinta zuwa ga shaiɗãnunsu,[1] sukan ce: "Lalle ne muna tãre da ku: Mu mãsu izgili, kawai ne."
[1] Kashi na hudu su ne Yahudãwa waɗanda suke sun san gaskiyar Annabcin Muhammadu da Manzancinsa, amma hãsada ta hana su su bi shi, sunã ƙõƙãrin ɓãta abin da ya zo da shi ta hanyar jħfa shibhõhi a ciki, dõmin su kange mutãne daga shigarsa. Sabõda haka aka ce musu shaiɗãnu. Duk wanda ya san gaskiya amma kuma ya yi girman kai daga binta, to, shi ne shaiɗan, daga aljannu kõ daga mutane.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net