Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 2 · Aya ta 129

Al-Baqara 2:129

البقرة

رَبَّنَا وَٱبْعَثْ فِيهِمْ رَسُولًا مِّنْهُمْ يَتْلُوا۟ عَلَيْهِمْ ءَايَـٰتِكَ وَيُعَلِّمُهُمُ ٱلْكِتَـٰبَ وَٱلْحِكْمَةَ وَيُزَكِّيهِمْ ۚ إِنَّكَ أَنتَ ٱلْعَزِيزُ ٱلْحَكِيمُ

Ma’ana

"Ya Ubangijinmu! Ka aiko, a cikinsu, wani manzo[1] daga gare su, yana karanta musu ãyõyinKa, kuma yana karantar da su Littãfin[2] da hikimar, kuma yana tsarkake su. Lalle ne Kai, Kai ne Mabuwãyi Mai hikima."

[1] Addu'ar an karɓa, ta aiko Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
[2] Littãfin-ya bayyana cewa Alƙur'ãni ne, dõmin bãbu wani sai shi. Hikima kuwa ita ce shari'ar da ke a cikinsa. Zai tsarkake su daga dauɗar shirka idan sun bĩ shi.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Baqara

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net