Al-Baqara 2:122
البقرةيَـٰبَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ ٱذْكُرُوا۟ نِعْمَتِىَ ٱلَّتِىٓ أَنْعَمْتُ عَلَيْكُمْ وَأَنِّى فَضَّلْتُكُمْ عَلَى ٱلْعَـٰلَمِينَ
Yã Banĩ Isrã'ĩla! Ku[1] tuna ni'imaTa wadda Na ni'imtar da ita a kanku, kuma lalle ne Nĩ, Nã fĩfĩtã ku a kan tãlikai.
[1] Kira na ƙarshe zuwa ga Yahũdu dõmin shiga Musulunci. An biyar da gargaɗi gare su da tunãtar da su cewa wannan addinin fa, shi ne addinin kãkansu Ibrãhim, dõmin kada su fanɗare daga addinin ubanninsu na ƙwarai. Kuma sunã da lãbãrin ginin Ɗakin Ka'aba da addu'ar da lbrahim ya yi alõkacin, wadda ta ƙunshi zuwan annabi daga cikin zuriyar Isama'ila a Makka, watau Fãrãna.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net