Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 2 · Aya ta 106

Al-Baqara 2:106

البقرة

مَا نَنسَخْ مِنْ ءَايَةٍ أَوْ نُنسِهَا نَأْتِ بِخَيْرٍ مِّنْهَآ أَوْ مِثْلِهَآ ۗ أَلَمْ تَعْلَمْ أَنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ قَدِيرٌ

Ma’ana

Abin da Muka shãfe[1] daga ãya, ko kuwa Muka jinkirtar da ita, zã Mu zo da mafi Alhẽri daga gare ta ko kuwa misãlinta. Ashe, ba ka sani ba, cẽwa lalle ne, Allah a kan dukkan kõme Mai ĩkon yi ne?

[1] Wannan ãya da abin da yakea bayanta sunã kõrewar shubuhãtu watau rikice-rikicen addini da maƙiyan addini suke sanyãwa a cikinsa, dõmin su sanya Musulmi a cikin shakka da ruɗu.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Baqara

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net