Maryam 19:81
مريموَٱتَّخَذُوا۟ مِن دُونِ ٱللَّهِ ءَالِهَةً لِّيَكُونُوا۟ لَهُمْ عِزًّا
Kuma suka riƙi gumãka,[1] baicin Allah, dõmin su kãsance mataimaka a gare su.
[1] Gunki, shi ne dukan abin bautawa wanda bã Allah ba. Wanda ya riƙi wani sãlihi ko malã'iki ko aljani, yanã bauta masa, to, yã riƙe shi gunki ke nan. Bauta ita ce bin umurni da barin hani. Wanda ya bi umurnin da bã na Allah ba, kõ ya bar abin banin da ba na Allah ba, to, ya bauta wa mai umurnin ko mai hanin, yã riƙe shi gunki baicin Allah.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net