Maryam 19:71
مريموَإِن مِّنكُمْ إِلَّا وَارِدُهَا ۚ كَانَ عَلَىٰ رَبِّكَ حَتْمًا مَّقْضِيًّا
Kuma bãbu kõwa daga gare ku sai mai tuzga mata.[1] Yã kasance wajibi ga Ubangijinka, hukuntacce.
[1] Idan an tãra mutãne dõmin hisabi, anã ajiye wuta a tsakãnin mutãne da Aljanna, Sa'annan a gitta sirãɗi a cikan wutar dõmin mutãne su bi akansa su ƙetare wutar zuwa Aljanna kuma waɗansu su fãɗa a cikin wutar dõmin azãba dawwamamma kõ kuma ta ɗan lõkaci gwargwadon laifi.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net