Maryam 19:5
مريموَإِنِّى خِفْتُ ٱلْمَوَٰلِىَ مِن وَرَآءِى وَكَانَتِ ٱمْرَأَتِى عَاقِرًا فَهَبْ لِى مِن لَّدُنكَ وَلِيًّا
"Kuma lalle nĩ, na ji tsõron[1] dangi a bãyãna, kuma mãtãta ta kasance bakarãriya! Sai ka bã ni wani mataimaki daga wajenKa."
[1] Amfãnin sãmu ɗã ga mutumin kirki shi ne dõmin ya gãji kirkin kuma ya taimaki sauran danginsa, ya rãyar da gida. Kuma wanda ba mutumin kirki ba yana yiwuwa ya sãmi ɗan kirki mai shiryar da shi zuwa ga hanyar ƙwarai.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net