Maryam 19:37
مريمفَٱخْتَلَفَ ٱلْأَحْزَابُ مِنۢ بَيْنِهِمْ ۖ فَوَيْلٌ لِّلَّذِينَ كَفَرُوا۟ مِن مَّشْهَدِ يَوْمٍ عَظِيمٍ
Sai ƙungiyõyin[1] suka sãɓã wa jũna a tsakãnins u. To, bõne ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta daga halartar yini mai girma.
[1] Bãyan ɗauke Annabin Allah Ĩsã ɗan Maryama ƙungiyõyin mutãne sun sãɓa wa jũnansu a cikin sha'aninsa. Yahũdu suna sũkar sa, Nasãra suka kasu uku: Nasũriyya suka ce: "Shi ɗan Allah ne" Malakaniyya suka ce: "Shi ne na uku ɗin uku," Ya'aƙũbiyya suka ce: "Shi ne Allah." Sabõda haka Nasara sukahaihaye kuma suka zurfafa, sa'an nan Yahũdu suka taƙaita kuma suka yi sũka gare shi.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net