Maryam 19:26
مريمفَكُلِى وَٱشْرَبِى وَقَرِّى عَيْنًا ۖ فَإِمَّا تَرَيِنَّ مِنَ ٱلْبَشَرِ أَحَدًا فَقُولِىٓ إِنِّى نَذَرْتُ لِلرَّحْمَـٰنِ صَوْمًا فَلَنْ أُكَلِّمَ ٱلْيَوْمَ إِنسِيًّا
"Sai ki ci kuma ki sha kuma ki ji sanyi ga idãnunki[1]. To, idan kin ga wani aya daga mutãne, sai ki ce, 'Lalle nĩ, na yi alwãshin azumi dõmin Mai rahama sabõda haka bã zan yi wa wani mutum magana ba."
[1] Jin sanyi ga idãnu shĩ ne farin cikin sabõda sãmun haihuwa. Ga ibãdar Banĩ lsrã'ĩla, mai azumi bã ya yin magana, amma ga Musulunci Allah Ya shãfe wannan hukunci. Mai azumi yanã magana sai dai anã son ya kãma bãkinsa daga maganar da bã ta ibãda ba.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net