Maryam 19:16
مريموَٱذْكُرْ فِى ٱلْكِتَـٰبِ مَرْيَمَ إِذِ ٱنتَبَذَتْ مِنْ أَهْلِهَا مَكَانًا شَرْقِيًّا
Kuma ka ambaci Maryamu[1] a cikin Littãfi, a lõkacin da ta tsallake daga mutãnenta a wani wuri, a gẽfen gabas.
[1] An fãra da ƙissar Maryamu dõmin a nũna sakamakon da aka yi mata da sãmun ɗan kirki sabõda kasancewarta mutumiyar kirki, kuma da nũna cewa Annabi Ĩsa bã ɗan Allah ba ne.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net