Al-Kahf 18:99
الكهفوَتَرَكْنَا بَعْضَهُمْ يَوْمَئِذٍ يَمُوجُ فِى بَعْضٍ ۖ وَنُفِخَ فِى ٱلصُّورِ فَجَمَعْنَـٰهُمْ جَمْعًا
Kuma Muka bar sãshensu a rãnar nan, yanã garwaya a cikin sãshe, kuma aka bũsa a cikin ƙaho sai muka tãra su, tãrãwa.[1]
[1] Allah Ya nũna yadda hãlin da Zulƙarnaini ya bar Yãjũj da Mãjũj, watau sun garwaya a cikin jũnansu, sa'an nan kuma wannan ma'anar aka bãyar da ita ga mutãne waɗanda ke bin son ransu, bã su bin shari'ar Allah, sunã hargitse a tsakãninsu, har a yi bũsar farko, su mutu, kuma a yi bũsa ta biyu su tãshi a cikin hargitsinsu, sai kuma a gitta Jahannama gaba gare su.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net