Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 18 · Aya ta 9

Al-Kahf 18:9

الكهف

أَمْ حَسِبْتَ أَنَّ أَصْحَـٰبَ ٱلْكَهْفِ وَٱلرَّقِيمِ كَانُوا۟ مِنْ ءَايَـٰتِنَا عَجَبًا

Ma’ana

Ko kuwa kã yi zaton cẽwa ma'abũta kõgo[1] da allo sun kasance abin mãmãki daga ãyõyin Allah?

[1] Lõkacin da Allah Ya ce: "kada Annabi ya wahalar da kansa dõmin baƙin cikin ba a karɓi maganarsa ba, sai Ya ba shi lãbãrin ma'abũta kõgo, yadda suka yi gudun hijira da addininsu, Allah Ya tsare su daga wahala, a cikin halin abin al'ajabi. Sa'an nan ƙissar ta tattara a kan ladubba waɗanda ake nħman Mutum ya tsare su tãre da Ubangijinsa a cikin dukan mõtsinsa, kamar yadda bayãni zai nũna.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Kahf

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net