Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 18 · Aya ta 88

Al-Kahf 18:88

الكهف

وَأَمَّا مَنْ ءَامَنَ وَعَمِلَ صَـٰلِحًا فَلَهُۥ جَزَآءً ٱلْحُسْنَىٰ ۖ وَسَنَقُولُ لَهُۥ مِنْ أَمْرِنَا يُسْرًا

Ma’ana

"Kuma amma wanda ya yi ĩmãni kuma ya aikata aikin ƙwarai to, zã mu yi sakamako a gare shi (watau kyauta) mai kyau[1], kuma zã mu gaya masa sauƙi daga umurninmu."

[1] Kyauta mai kyau a nan ba Aljanna ba ce, dõmin maganar ta Zulƙarnaini ce idan ya ci ƙasa, yanã iya sanya mãsu ĩmãninta a cikin hãli mai kyau. Amma idan an ɗauki maganar, ta Allah ce, a cikin maganar Zulƙarnaini ga kãfiri, to, a nan 'mai kyau' sai ta zama Aljanna ke nan.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Kahf

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net