Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 18 · Aya ta 76

Al-Kahf 18:76

الكهف

قَالَ إِن سَأَلْتُكَ عَن شَىْءٍۭ بَعْدَهَا فَلَا تُصَـٰحِبْنِى ۖ قَدْ بَلَغْتَ مِن لَّدُنِّى عُذْرًا

Ma’ana

Ya ce: "Idan na tambaye[1] ka daga wani abu a bãyanta, to, kada ka abũce ni. Lalle ne, kã isa ga iyakar uzuri daga gare ni."

[1] Mũsã ya kãsa yin haƙuri a bãyan ya yi alkawura cewa zai yi haƙuri, sabõda ba yã halatta ga mutum ya ga abin da ya sãɓa wa shari'a, sa'an nan ya yi shiru. Dã zai halatta a yi shiru, dã Mũsã bai yi magana ba ga aikin mãlamin da Allah Ya umurce shi da ya tafi ya karɓo ilmi daga gare shi, a bãyan Yã gaya masa cewa,Yã bã shi wani ilmi daga gare shi. Dõmin sharaɗin da ya sãɓa wa shari'a warwararre ne. Sabõda haka Allah bai zargi Mũsa ba a bayan sun rabu. Sake al-munkar wãjibi ne a cikin ladubban shari'a gwargwadon hãli, kamar yadda yake a cikin Hadĩsi. Ana gabãtar da hukuncin da ya fi tsanani.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Kahf

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net