Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 18 · Aya ta 7

Al-Kahf 18:7

الكهف

إِنَّا جَعَلْنَا مَا عَلَى ٱلْأَرْضِ زِينَةً لَّهَا لِنَبْلُوَهُمْ أَيُّهُمْ أَحْسَنُ عَمَلًا

Ma’ana

Lalle ne Mũ, Mun sanya abin da ke kan ƙasa wata ƙawa[1] ce gare ta, dõmin Mu jarraba su; wanne daga cikinsu zai zama mafi kyau ga aiki.

[1] Sabõda haka ƙawar ƙasa, kamar furen itãcenta ne, bã su ruɗin mai hankali ga tsarewar ladabi tãre da Ubangijinsa, da bin sharĩ'ar Littafin da aka saukar wa Annabi kuma ba a sanya masa karkata ba.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Kahf

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net