Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 18 · Aya ta 65

Al-Kahf 18:65

الكهف

فَوَجَدَا عَبْدًا مِّنْ عِبَادِنَآ ءَاتَيْنَـٰهُ رَحْمَةً مِّنْ عِندِنَا وَعَلَّمْنَـٰهُ مِن لَّدُنَّا عِلْمًا

Ma’ana

Sai suka sãmi wani bãwa daga bãyin Mu, Mun bã shi wata rahama[1] daga wurin Mu, kuma Mun sanar da shi wani ilmi daga gun Mu.

[1] Rahama a nan ita ce Annabci sabõda cħwa kuma an bã shi ilmi daga gun Allah, kuma ya yi hukunci da shi. Ilmin ilhãma bã a yin hukunci da shi dõmin Annabãwa kawai Allah Ya tsare daga kuskure game da wahayi. Wannan ne bambanci bayyananne a tsakanin wahayin Annabci da wahayin walicci. Haka mu'ijiza da karãma, su duka sãɓãwar al'ada ne, amma mu'ujizar Annabi an san zã ta zo daga bãkin wanda aka yi dõminsa, amma karãma bãbu mai saninta, sai tã auku. Sabõda waliyyi bã ya iya yin tãkara, amma annabi yana iya yin tãkara a kan maƙiyansa.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Kahf

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net