Al-Kahf 18:60
الكهفوَإِذْ قَالَ مُوسَىٰ لِفَتَىٰهُ لَآ أَبْرَحُ حَتَّىٰٓ أَبْلُغَ مَجْمَعَ ٱلْبَحْرَيْنِ أَوْ أَمْضِىَ حُقُبًا
Kuma a lõkacin da Mũsã[1] ya ce wa yãronsa, "Bã zan gushe ba sai na isa mahaɗar tẽku biyu, kõ in shũɗe da tafiya shekara da shẽkaru."
[1] Shĩ ne MũSã bn Imrãn Manzon Banĩ Isrã'ĩla. Sababin wannan ƙissa, an tambaye shi ne, "Wãne ne ya fi ilmi a saninsa?" Sai ya ce: "Shĩ ne ya fi. Wannan jawãbi nãsa gaskiya ne, dõmin shĩ ne Manzon zãmaninsa, shĩ ne aka bai wa Attaura, kuma Allah Ya yi magana da shi, sai dai ya mance bai ce Allah Ya fi sani ba, dõmin haka aka ce masa ya tafi neman ilmi ga wani mutum a magamar teku biyu. Wannan bãwan Allah Haliru ne. Yãron Mũsã kuwa, shĩ ne Yũsha'u bn Nũn, Manzon Allah a bãyan Mũsã. Kĩfin kuma na guzurinsu ne wanda Allah Ya umurce shi ya ɗauka, sõyayye, kuma aka ce musu duka inda yai rai, to, a nan ne Bãwan Allah yake, mai shirin ƙãra wa Mũsã ilmi. Mayar da ilmi ga Allah, shĩ ne ladabin shari'a.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net