Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 18 · Aya ta 58

Al-Kahf 18:58

الكهف

وَرَبُّكَ ٱلْغَفُورُ ذُو ٱلرَّحْمَةِ ۖ لَوْ يُؤَاخِذُهُم بِمَا كَسَبُوا۟ لَعَجَّلَ لَهُمُ ٱلْعَذَابَ ۚ بَل لَّهُم مَّوْعِدٌ لَّن يَجِدُوا۟ مِن دُونِهِۦ مَوْئِلًا

Ma’ana

Kuma Ubangijinka Mai gãfara ne, Ma'abũcin rahama. Dã Yanã kãma su sabõda abin da suka sanã'anta, lalle ne, dã Ya gaggauta azãba a gare su. Ã'a, sunã da lõkacin alkawari, (wanda) bã zã su sãmi wata makõma ba, baicinSa.[1]

[1] Watau ba su da wata makõma su bar wannan lõkacin alkawarin saukar azãbar.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Kahf

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net