Al-Kahf 18:55
الكهفوَمَا مَنَعَ ٱلنَّاسَ أَن يُؤْمِنُوٓا۟ إِذْ جَآءَهُمُ ٱلْهُدَىٰ وَيَسْتَغْفِرُوا۟ رَبَّهُمْ إِلَّآ أَن تَأْتِيَهُمْ سُنَّةُ ٱلْأَوَّلِينَ أَوْ يَأْتِيَهُمُ ٱلْعَذَابُ قُبُلًا
Kuma bãbu abin da ya hana mutãne su yi ĩmãni a lõkacinda shiriya ta zo musu, kuma su nẽmi gãfara daga Ubangijinsu, fãce hanyar farko[1] ta je musu kõ kuma azãba ta jẽ musu nau'i-nau'i.
[1] Hanyar farko ita ce Allah Ya halaka su sabõda laifinsu kõ kuma azãba ta je musu nau'i-nau'i, dõmin su musulunta sai ƙarshe idan sun ƙi a halaka su. Waɗansu sun fassara 'ƙubala' ko 'ƙibala' da ta fuskance su bayyane, bisa ga karãtun kalmar 'ƙibala' da wasalin ƙasa, da ma'anar azaba.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net