Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 18 · Aya ta 52

Al-Kahf 18:52

الكهف

وَيَوْمَ يَقُولُ نَادُوا۟ شُرَكَآءِىَ ٱلَّذِينَ زَعَمْتُمْ فَدَعَوْهُمْ فَلَمْ يَسْتَجِيبُوا۟ لَهُمْ وَجَعَلْنَا بَيْنَهُم مَّوْبِقًا

Ma’ana

Kuma da rãnar da Allah Yake cẽwa, "Ku kirãyi abõkan tarayyãTa, waɗanda kuka riya." Sai su kirãye su, sai bã zã su karɓa musu ba, kuma Mu sanya Maubiƙa[1] (Mahalaka) a tsakãninsu,

[1] Maubiƙã sũnan wani rãfi ne na wuta, asalinsa daga 'Wabiƙa,' wãtau yã halaka. Za a sanya wannan rãfi a tsakãnin mãsu bin Shaiɗan da sũrõrin gumãka, da wanda ya shirya musu gumãkan, sunã bauta musu.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Kahf

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net