Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 18 · Aya ta 50

Al-Kahf 18:50

الكهف

وَإِذْ قُلْنَا لِلْمَلَـٰٓئِكَةِ ٱسْجُدُوا۟ لِـَٔادَمَ فَسَجَدُوٓا۟ إِلَّآ إِبْلِيسَ كَانَ مِنَ ٱلْجِنِّ فَفَسَقَ عَنْ أَمْرِ رَبِّهِۦٓ ۗ أَفَتَتَّخِذُونَهُۥ وَذُرِّيَّتَهُۥٓ أَوْلِيَآءَ مِن دُونِى وَهُمْ لَكُمْ عَدُوٌّۢ ۚ بِئْسَ لِلظَّـٰلِمِينَ بَدَلًا

Ma’ana

Kuma a lõkacin da Muka ce wa malãiku, "Ku yi sujada ga Ãdamu." Sai suka yi sujada fãce Iblĩsa, yã kasance daga aljannu sai ya yi fãsiƙanci ga barin umurnin Ubangijinsa, To fa, ashe, kunã riƙon sa, shi da zũriyarsa, su zama majiɓinta baicin Ni, alhãli kuwa su maƙiya ne a gare ku? Tir da ya zama musanya ga azzãlumai.[2]

[2] Allah Shĩ ne Ya halitta mutãne, kuma Ya ɗaukaka darajarsu, dõmin Yã sanya malã'iku su yi sujada ga ubansu Ãdamu. Sabõda wannan sõyayyar kuma Ya bã su sharĩ'ar da zã su bi su shiryu har su shiga Aljanna, amma sai suka ƙi, suka kõma wa Shaiɗan wanda yake shi ne farkon maƙiyin ubansu, Ãdamu, wanda ya ƙi yi wa sujada, har aka la'ane shi, sunã bin sa, shi da ɗiyansa, alhãli kuwa bãbu wani abin da zã su iya yi musu na alheri ko na sharri, dõmin sũ ma halitta ne kamarsu. Bã su san kõme ba a sama kõ a ƙasa, kuma Allah bã Ya yin ma'amalar kõme da su. Wanda ya bi Shaiɗan ya bar Allah, to, yã yi mugunyar musanya, kuma yã zãlunci kansa ƙwarai.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Kahf

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net